Tuesday, 14 November 2017

Kasar italiya bazata je gasar cin kofin Duniya ba a karin farko cikin shekaru sittin

Kasar Italiya bazata je gasar cin kofin kwallon Duniya ba da za'a buga a kasar Rasha idan Allah ya kaimu shekara me zuwa, hakan kuwa ya farune dalilin rashin nasarar da tayi a wasan da suka buga ita da Sweden jiya, wanda suka tashi babu wanda ya zura wa wani kwallo a raga.Sweeden din dai tayi nasara akan Italy ne da kwallo daya data zurata mata a raga a wasansu na farko.

Wannanne karo na biyu a tarihin kasar Italiya sannan kuma na farko a cikin shekaru sittin da suka gabata (watau tun shekarar 1958) da bata samu zuwa gasar cin kofin kwallon kafa na Duniya ba.

Italiya dai ta taba lashe kofin Duniya har sau hudu a tarihi kuma wasu na ganin rashin ta a gasar cin kofin Duniyar badi, watakila ya ragewa gasar armashi.

No comments:

Post a Comment