Thursday, 2 November 2017

Kasar Jamus zata samar da wutar lantarki fiye da wadda mutane ke bukata: Za'a biya mutane kudi dan suyi amfani da wutar lantarkin

wind-turbine.jpg
Wata miyar sai a makwabta, a ranar lahadin data gabatane wani kamfanin dake samar da wutar lanatarki a kasar Jamus ta hanyar iska yayi kintacen cewa za'a samu iska fiye da kima a wancan lokacin wanda hakan zai haifar da samar da karfin wutar lantarki fiye da yanda mutane ke bukata, kamar yanda kafar watsa labarai ta Bloomberg ta ruwaito.


Idan kuwa aka samu wutar lantarki fiye da yanda mutane ke bukata to kudin wutar zai yi kasa sosai yanda dole saidai kamfanin ya roki mutane suyi amfani da wutar lantarkin ya biyasu kudi ko kuma ya dakatar da aikin samar da wutar lantarkin.

A shekarun baya lokacin fasahar samar da wutar lantarki ta iska me kadawa bata dade da fitowaba tsarata da kula da kayan aikinta yana da tsada sosai to amma yanzu abin yayi sauki kuma kasar Jamus din tana sahun gaba a kasashe masu samar da hasken lantarki ta iska me kadawa.

Wannan labari ya dauki hankulan Duniya gaba daya bama Najeriya kawai ba, kasashen da sukaci gaba sunyi sharhi akan wannan labari da cewa ai ya kamata ace kamfanin yana da wani tsari na kota kwana irin wannan, ya kuma samar da wasu injina kokuma batura da zasu iya ajiye wutar a lokacin da aka samu wutar da ta wuce wadda za'a iya amfani da ita.

A kasashe masu tasowa irin Najeriya kuwa mutane sun cika da mamakine inda aka rika fadin Allah sarki mu gashi da kudin mu muna biyan kudin wutar amma an hanamu, kusan duk lokacin da kake aiki da wuta baka da tabbacin zaka gama aikin ba tare an dauke wutarba amma ga wasu can su biyansu ma ake suyi amfani da wutar.

No comments:

Post a Comment