Thursday, 30 November 2017

KASASHEN TURAWA BAKWAI IZALA ZA SU ZIYARTA

Malaman Izala suna ci gaba da gudanar da Da'awa a yankin Turai tare da samun gagarumar Nasara.

Shugaban IZALA Sheikh Abdullahi Bala Lau, tare da sakataren kungiyar Sheikh Kabiru Gombe ne suka samu gayyata daga wasu Kungiyoyin Ahlussunnah dake yankin na Turai.


Kungiyar dai tana samun gagarumar Nasara a kasashen Duniya, ganin yadda mafiya yawan Kungiyoyin Ahlussunnah dake  kasashen Duniya suke neman kulla abota da kungiyar. A yanzu kungiyar Tayi yi wa'azuzzuka a kasashen Burtaniya, Greece, da Jamus, inda nan gaba zata shiga cikin kasashen Belgium, Holland, Italy, Spain insha Allah.

No comments:

Post a Comment