Friday, 10 November 2017

Kungiyar Bayern Munich Za Ta Gina Masallaci A Filin Kwallonta


Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich dake kasar Jamus za ta gina masallaci a filin kwallonta mai suna Allianz Arena.

Masallacin zai kasance na farko a duniya da aka gina a filin kwallo.
Rahotanni sun nuna cewa gina masallacin ya biyo bayan bukatar da dan kwallon kungiyar Frank Ribery ya mikawa hukumar gudanarwar kungiyar ne na ganin an sama wa shi da sauran musulman 'yan kwallon kungiyar waje don ganin suna gudanar da ibada a ranakun wasa da kuma na atisaye.

Saidai mika koken ya zo da bazata, inda hukumar gudanarwar kungiyar ta amince da bukatar ta soma gina katafaren masallaci wanda musulmai 'yan wasa da magoya bayan kungiyar za su dinga gudanar da ibadar su. Inda za a samar da limami da kuma ofishin da zai dinga kula da masallacin.

Hukumar gudanarwar kungiyar za ta bada kashi 85 na kudin gina masallacin, yayin da kaso 15 din za a karbi gudummawa ne daga 'yan wasa da magoya bayan kungiyar.

No comments:

Post a Comment