Saturday, 18 November 2017

Kyan Alkawari cikawa: Kalli dakin shan magani da uwargidan shugaban kasa Haj. Aisha Buhari ta gina a garin Daura

Wannan dakin shan maganine na mata masu ciki da uwargidan shufaban kasa Hajiya A'isha Buhari ta gina a cikin asibin gwamnati(General Hospita) dake garin Daura, mahaifar shugaban kasan.Hajiya A'isha Buhari ta guna wannan dakin shan maganine a karkashin gidauniyarta me suna Future Assured kuma ta mika wannan dakin shan magani ga gwamnatin jihar Katsina dan ta ciigaba da kula dashi.

Tun a kwanankin bayane uwargidan shugaban kasar tayi alkawarin gina wannan dakin shan magani kuma gashi Allah ya bata ikon cikawa.

Muna mata fatan Allah ya saka mata da Alheeri.

No comments:

Post a Comment