Sunday, 19 November 2017

Labarin matar da kishi yasa ta kashe mijinta, bayan taga sakon waya a wayarshi

Wannan labarin ma'aurata ne daya karade shafukan sada zumunta da muhawara na yanar gizo, Bilya Bello Halliru, da a gurin tsohon shugaban jam'iyyar PDP watau Bello Halliru, ya gamu da ajalinsa bayan da matarshi, Maryam Sanda ta caccaka mishi wuka, saboda tsabar kishi, bayan da taga wani sakon waya na wata budurwarshi, kamar yanda rahotanni suka bayyana.
A kwanakin baya sun taba samun rikici wandashima har ta cijeshi a kunne, yaje Asibiti aka mai magani, tun daga wancan lokaci an rika bashi shawarar ya bar gidan amma ya kiya.
Ma'auratan suna da suna da diya da Allah ya albarkacesu da ita. Wadannan hotunan lokacin da sukayi aurene kuma soyayyarsu tana cikin ganiyar dadinta.
Mun fatan Allah ya jikan Halliru yakai Rahama kabarinshi.

No comments:

Post a Comment