Wednesday, 1 November 2017

Mace, soja, bahaushiya ta farko data kai babban mukamin Wing commander a aikin sojan sama

Hajara Diyace gurin marigayi Marafan birnin Kudu, Colonel Bashari Umaru daga karamar hukumar Birnin Kudu ta jihar Jigawa, itace shugabar bangaren jiyya ta asibitin sojoji dake Kano, ta halarci yaki a kasar Congo ta kuma yi aiki a Ibadan, Kaduna da sauran wasu jihohi, itace mace bahaushiya ta farko dake rike da babban mukamin Wing commander a aikin sojan sama.


An haifi Hajara a Dorayi quarter ranar 14 ga watan Maris na shekarar 1964, ta taso a Yakasai Quarters,, Tayi karatu a makarantar koyan aikin jiyya dake Kano, bayan ta kammala makarantarne ta shiga aikin sojan sama, a lokacin da taji ana daukar sojoji ma'aikatan jiyya.

Da take bayar da labarin yanda akayi ta shiga aikin soja, tace mahaifiyarta bata son tayi aikin soja, haka kuma babanta ya nuna bayaso dan ya farantawa mahaifiyarta rai amma a zahiri ya karfafa mata gwiwa akan tayi aikin sojan.

No comments:

Post a Comment