Monday, 6 November 2017

Mai dokar bacci: Motar jami'an kula da titi naci da wuta: hakan ya jawo cece-kuce

Wannan hoton motar ma'aikatan gwamnatin tarrayane dake kula da lafiyar titi da duba ababen hawa da ake kira da Road Safety a takaice, take ci da wuta akan titi, hoton ya dauki hankulan mutane sosai a shafukan sada zumunta da muhawara inda mutane suka rika fadin kunga motarsu naci da wuta basu kasheta ba amma idan suka tare mutum akan hanya sai su rikatambayarshi ina abin kashe wutarshi yake.

Shidai wannan hoto ba'a tantance yaushe aka daukeshiba ko kuma a inane aka daukeshiba amma ya ja hankulan mutane sosai.

No comments:

Post a Comment