Monday, 27 November 2017

Makarantar Firaimare kamar Jami'a: Daya daga cikin makarantun firaimare da gwamnatin jihar Borno ke ginawa kenan

Jihar Borno ta sha fama da hare-haren mayakan kungiyar Boko haram wanda ya hada da kone gidaje da makarantu da mayakan sukeyi a duk garin da suka kai hari, duk yanzu ma ana samun hare-haren nan da can, amma ba kamar a bayaba, Gwamnatin jihar ta karkashim gwamna Kashim Shattima ta fara ayyukan sake gina wasu makarantun da kuma sabbi guda 21.

Wannan makarantar firaimare ce, daya daga cikin wadanda Gwamnatin jihar ta Bornon ke ginawa, me hawa biyu, irin wannan gini haka, abin ya kayatar, dan kuwa ko wata jami'ar sai haka, kamar yanda wani bawan Allah ya saka hotunan a dandalinshi na sada zumunta da muhawara yayi ikirarai. 
No comments:

Post a Comment