Thursday, 23 November 2017

Masana'antar fim ta kudu zata karrama Ali Nuhu

Za'a karrama Tauraron fina-finan Hausa Ali Nuhu (Sarki) a masana'antar fim ta kudancin kasarnan, taron karrama jaruman da ake shiryawa duk shekara da akawa lakabi da BON a takaice, zai baiwa Ali Nuhun kyautar karramawa ta jarumi na musamman.

Za'a yi wannan taronne ranar 16 ga watan Disamba idan Allah ya kaimu.

Masu bayar da kyautar sun bayyana Ali Nuhu a matsayin jiko kuma abin koyi ga matasa da yawa a Arewa da suke da burin shiga masana'antar ta finafinan kudancin kasarnan, dan hakane za'a bashi kyautar.

Muna tayashi murna.

No comments:

Post a Comment