Sunday, 19 November 2017

Mata na aikin sayar da nama

A jiyane mukaji labarin wata baiwar Allah da take aikin jiwa maza aski, to yauma ga wasu mata masu aikin fawa, sayar da nama a jihar Naija, wannan aiki dai kusan za'ace aikin mazane amma ga dukkan alamu wadannan matan suma sun dauki haramar nunawa maza cewa duk fa abin da zasu yi to suma zasu iyayi.

Koda idan ka kalli bayan matan a cikin wannan hoto zaka iya hango duk mazane abokan sana'ar tasu.

Hoto daga rariya.

No comments:

Post a Comment