Tuesday, 21 November 2017

Matar da ta kashe mijinta: Abubuwan fadakarwa da barkwanci da mutane suka rika fada: Kashi na DAYA

Tun bayan faruwar lamarin kisan da Maryam ta yiwa mijinta Bilya mutane sunyi ta kiraye-kiraye ga iyaye, ma'aurata maza da mata da ma samari akan kula da tarbiyya da kuma neman ilimi da kuma kula da irin matar da mutum zai aura, bayan kiraye-kirayen jawo hankalu, wannan labarin ya bude babi na fadakarwa a fakaice da kuma barkwanci tsakanin mutane.

Misali maganarnan ta sama da akeganin hotonta wani bawan Allahne yayita a dandalinshi na sada zumunta da muhawara na shafin Twitter kuma abinda ya rubuta din ya matukar dauki hankulan mutane sosai.

Ga ra'ayoyin mutane akan wannan magana da wannan bawan Allah yayi.
No comments:

Post a Comment