Friday, 24 November 2017

Matar da ta kashe mijinta, Maryam ta bayyana a gaban kotu rike da kur'ani

Maryam Sanda kenan matar da ake zargi da kashe mijinta Bilya ta hanyar daba mishi kwalba, anga maryam rike da kur'ani da kuma carbi da diyarta, ta lullube kanta yanda ba'a iya ganin fuskarta, a zaman kotu da akayi yau a Abuja kamar yanda bbchausa ta ruwaito.


Maryam taki amsa laifin kashe mijinta da aka zargeta dashi, kuma lauyanta ya nemi a bayar da belinta amma alkali ya hana, an bayar da umarnin tsareta a gidan yari, kuma an daga shari'ar zuwa ranar bakwai ga watan Disamba.
Allah shi kyauta, ya rabamu da aikin dana sani.

No comments:

Post a Comment