Friday, 3 November 2017

Matashiya ta fito neman kujerar Sanata a jihar Bauchi

Labarin wannan matashiyar me suna Ziyaatulhaq Usman Tahir ya karade shafukan sada zumunta da muhawara bayan data fito ta bayyana aniyarta ta neman takarar kujerar sanata ta bauchi da kudu a zaben shekarar 2019 idan Allah ya kaimu, ta bayyana cewa sananniyar me sayar da kayan mata ta yanar gizo wadda akewa lakabi da Jarumace zata dauki nauyin wannan takara tata, kuma.

 Kwanan nan ne dai majalisar tarayya ta saka wani kudiri cikin doka da zai baiwa matasa damar fitowa neman mukaman siyasa kuma Ziya'atutayi amfani da wannan damane wajan bayyana wannan aniya tata.
Ziya'atu ta bayyana irin abubuwan da take da burin yiwa mazabarta idan suka zabeta a wannan kujera kamar haka:

Mazabar Bauchi ta kudu ku fito ku zabi Ziyaatulhaq Usman Tahir.

Ilimi kyauta

Zata daukewa iyaye kayan daki na 'ya'ya mata idan sun tashi yin aure.

Zata rika baiwa iyaye mata albashin dubu dari kowane wata ladan tarbiyyar da sukewa 'ya'ya.

Zata hana 'ya 'ya mata talla.

Duk wanda aka kama yayi fyade za'a mishi sabuwar kaciya kuma a kulleshi a gidan yari na tsawon shekaru ashirin da biyar.

Zata aurar da zawarawa aure na mutunci.

Zata tallafawa marayu har karshen rayuwarsu.

Tace idan ta samu wannan kujera to bazata yarda ta saukaba ba tare da ta gyara mazabarta ta Bauchi ta kudu ba.

A cikin wadanda sukayi sharhi a dandalinta na sada zumunta da muhawara Wani ya tambayeta yana fatan idan aka kirata aka bata kudi bazata janye wannan buri nata ba kuma zata jajirce wajan yin gogayya da wadanda ake ganin tsoffin hannune a siyasar zamani?

Ta bashi amsar cewa babu kudin da zasu sa ta canja ra'ayinta, zata yi iyayinta har sai abinda Allah yayi.

No comments:

Post a Comment