Tuesday, 21 November 2017

Mutumin da ya gano maganin cutar bacci kuma kwamishinan Ilimi na jihar Kaduna Farfesa Andrew Nok ya mutu

Kwamishinan Ilimi na jihar Kaduna, Farfesa Andrew Jonathan Nok ya mutu yau bayan gajeruwar rashin lafiya, a lokacin rayuwarshi ya kafa tarihin da Duniya ba zata taba mantawa dashiba, shine mutum na farko a Duniya da ya fara gano maganin ciwon bacci wanda a turance ake kira da (Sleeping Sickness).

Wannan bajinta da ya nuna ta sa Duniya ta karramashi.

Lallai jihar Kaduna da Najeriya Anyi rashi.

No comments:

Post a Comment