Sunday, 12 November 2017

"Mutane har daga Arewa nata damuna in sake tsayawa takarar shugaban kasa">>Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana cewa yana ta samun jama'a na ziyartarshi daga sassa daban-daban na kasarnan suna rokonshi ya sake tsayawa takara, ya kara da cewa abinda yafi taba mai zuciya shine idan ya shiga taron Jama'a zakaji mutane nata shewar ka dawo goodluck! Ka dawo goodluck, yace irin wannan yana sashi ya zubar da hawaye.


Ya bayyana hakane lokacin da yake hira da sanannen da jaridarnan Dele Momodu amma ya kara da cewa maimakon yaji wani matsayi da girman kai ya shigeshi a duk lokacin da irin haka ta faru yakan tuna irin kurakuran da ya yayi a baya sai yaji bai kamata yayi dagawa ba.

Ya kara da cewa bai san abin da Allah ya boye ba amma gaskiya akwai matukar wuyar gaske ya sake tsayawa takarar shugabancin kasar nan, ya bayar da iya gudumuwarshi, zai koma gefe ya ci gaba da rayiwarshi.

Yace shi ko tafiye-tafiye be cika yi ba saboda tsadar tikiti.

No comments:

Post a Comment