Wednesday, 29 November 2017

Ranar shida ga watan Disamba Shugaba Buhari zaikai ziyarar aiki jihar Kano>>Gwamna Ganduje

Bayan da ga watan Nuwamba da ake ta dakon zuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari jihar Kano ya zo karshe, Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa shugaba Buharin zai kai ziyarar kwanaki biyu jihar ta Kano ranar shida ga watan Disamba me kamawa.

Gwamnan ya kara da cewa a lokacin ziyarar tashi, Shugaba Buharin zai duba tare da kaddamar da wasu manya-manyan aikin raya kasa da gwamnatin jihar tayi.

Yanzu haka dai shugaba Buharin yana can kasar Kwadebuwa inda yake halartar taron gamayyar kungiyoyin tarayyar turai da na Afrika.

No comments:

Post a Comment