Wednesday, 1 November 2017

Rigar sulke da aka kera a kasar Rasha da makamin nokiliya baya yiwa sojan dake sanye da ita komai

TUS_3142_1
Wannan wata rigace ta musamman da wani kamfanin kasar Rasha me suna Corporation Rostec ya kera wadda aka sakawa sunan Ratnik-3, ita wannan riga kamar yanda wanda ya kerata ya bayyana cewa ta sojojice kuma idan soja yana sanye da ita zata bashi kariya daga harin makamim kare dangi na nokiliya, dama dukkan wani irin bam me tarwatsewa, ruwa ko wata girgiza me karfi bazata yiwa sojan dake sanye da ita komaiba, akwai abubuwa daban-daban dake tare da wannan rigar sulke.


GettyImages-477453670
Abu na farko muhimmi dake tattare da wannan riga itace wannan sabuwar bindigar da ake kallon hotonta a sama, ita wannan bindiga sunanta AK-12, kuma an yitane dan ta maye sananniyar bindigar nan wato AK-47 wadda injiyan hada kayan sojoji Mikhail Kalashnikov ya kera, itama wannan kamfaninshine ya kerata.

Haka kuma ita wannan riga tana tattare da abun da soja zai iya harba gurneti dashi, idan hakan ta kama da kuma wasu abubuwan dake taimakawa jikin dan adam ya rayu, koda ace za'a samu wani yanayi da soja zai iya dadewa sanye da ita, akwai na'urorin sadarwa da kuma kwamfutoci kala-kala, akwai kariya ga jikin dan Adam kala-kala da kuma wasu abubuwan amfani hamsin da tara duk a jikin wannan riga.

Ita wanna riga dai tana baiwa jikin soja kariya kusan kashi casa'in cikin dari, kuma duk wani harbin makami ko kuma bindiga da za'a yi akai-akai kuma kusa da sojan dake sanye da ita babu abinda zai sameshi.
Stunt performer Viktoria Kolesnikova takes part in endurance testing of a new army watch, designed by Russia's Rostec Corporation, at the range of TsNIITochMash (the Central Scientific and Research Institute for Precision Machine Engineering, Rostec's subsidiary). The watch is resistant to high impact, electromagnetic effect, electronic warfare actions, and consequences of a nuclear blast. The watch is to be included in the Ratnik combat gear for Russia's ground, airborne, coastal defence troops, and other forces. 

Yanzu haka dai an samu wani dan kasada ya saka wannan rigar anyi gwajin makamai kala-kala a jikinshi amma batayi komai ba, wannan hoton na sama yana nuna lokacin da ake yin gwajin rigar sulkenne.

Yanzu haka dai wasu masu sharhi akan lamurran kere-keren makaman Duniya sun gargadi kasar Amurka da ta dage itama tayi wani abu makamancin wannan ko kuma ma wanda yafi wannan saboda nan gaba kada kasar Rashar ta zamar mata barazana.
Photos:Getty Images 

No comments:

Post a Comment