Thursday, 2 November 2017

Ronaldo ya bayyana dalilin da yasa Tottenham tayi nasara akansu

Cristiano Ronaldo ya bayyanawa manema labarai dalilin da ya sa kungiyarshi ta Real Madrid ta sha kashi a hannun Tottenham da ci 3- a wasan cin kofin zakarun turai da aka buga jiya Laraba, Ronaldon yace alkalin wasane ya ci su domin kuwa be musu adalci ba a kwallaye biyun farko da Tottenham ta saka musu a raga saboda duka anyi satar gidane aka cisu.Shima dai Ronaldon ya fadi irin maganar da kocin su Zidane ya fada cewa, basu natsu suka buga wasa ba kamar yanda aka sansu, ya kara da cewa amma har yanzu lokaci be kure musu ba na su kara himma wajan ganin sun dawo da kwazon da aka sansu dashi.

Ronaldo yace duk da yake sun saba da yin nasara a mafi yawancin wasannin da suke bugawa amma wannan rashin nasara da sukayi bai dagamai hankali ba saboda yana da yakinin nan gaba zasu dawo da kwarjininsu.

No comments:

Post a Comment