Sunday, 19 November 2017

Sanata na kwakular Hanci: Wannan hoton ya dau hankulan mutane

Wannan hoton na sanata Shehu Sani yana jawabi a gaban majalisar Dattijai ya dauki hankulan mutane sosai, an dauki hoton a kan gaba, ga wani sanata can ta gefen sanata Shehu Sanin yana kwakular hanci, abinda wasu ke ganin cewa abin kunyane mutum ya rika yin hakan a bainar jama'a.

Haka kuma ta dayan gefen nashi akwai wani sanatan yana waya amma yanayin yanda ya rike wayar kamar ya sakawa Sanata Shehu Sanin wayar a kunnenshine yana waya.

Hoton ya dauki hankulan mutane sosai inda akayi ta maganganu kala-kala.

No comments:

Post a Comment