Friday, 10 November 2017

Shawarwarin rayuwa daga Malam Aminu Ibrahim Daurawa


SHAWARA CE👌🏽

Don Allah kada a hada kai da kai a zalunci wani.

SHAWARA CE👌🏽

Ka yi aikin kirki, domin duniya ba matabbata ba ce.

SHAWARA CE👌🏽
Ka tsaya a kan gaskiya, duk rintsi duk wahala.SHAWARA CE👌🏽
In ka ga wasu suna husuma, yi iya bakin qoqarinka ka sasanta, sai dai  in abin ya fi qarfinka.

SHAWARA CE👌🏽
Ka guji hassada, domin bayan haddasa gaba dazatayi tsakanin ka da dan'uwanka, zata kuma cinye ayyukan ka.

SHAWARA CE👌🏽
Ka rike girmanka da Allah ya ba ka, domin ba dabaranka ne yakawo maka girman ba.

SHAWARA CE👌🏽
Kadauki na sama dakai a matsayin iyayenka, sa'anninka a matsayin abokanka, na kasa dakai a matsayin 'ya'yanka.

SHAWARA CE👌🏽
Shiga haqqin mutane ba shi dakyau, Allaah ne Ya hana, ka guji yin hakan, domin zai kaika ga halaka.

SHAWARA CE👌🏽
Kada kayi don ka faranta ko munana wa wani, kada kuma kayi dan wani, domin ba shine ya halicce ka ba .

Allah ya bamu ikon dauka

No comments:

Post a Comment