Friday, 24 November 2017

Sheikh Kabir Gombe ya bayyana dalilin da yasa yafi yiwa mata wa'azi

A cikin satinnan da muke cikine shugaban kungiyar Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau da Sheikh Kabir Gombe suka tafi kasar Ingila dan yin wa'azi acan, bayan sun isa kasar Ingilar sun kaiwa bbchausa ziyara inda har akayi hira dasu.

A cikin hirar an tambayi Sheikh Kabir Gombe ko me yasa yake yiwa mata wa'azi?

Sai ya bayar da amsar cewa akwai gurare da yawa a Alkur'ani inda Allah idan ya ambato Namiji saiya ambaci mace, kuma mata sune sukafi bukatar Ilimi saboda sune ke renon al'umma amma mafi yawanci ba'a cika kula da hakan ba shiyasa ya mayar da hankali wajan yi musu wa'azi.

Domin jin cikakkiyar amsar da Sheikh Kabir Gombe ya bayar sai a kalli hoton bidiyon sama.

No comments:

Post a Comment