Wednesday, 22 November 2017

"Shekaru goma da aure amma har yanzu baki daina zugashiba?">>Wani ya gayawa Mansurah Isah bayan data yiwa mijinta kirari da "me buhu-buhun masara da dawa"

Tsohuwar tauraruwar finafinan Hausa kuma mata a gurin Tauraron finafinan Hausa Sani Musa Danja, Zaki, watau Mansura Isah kenan a wannan tsohon hoton nasu, Mansura ta yiwa mijinta kirari sosai inda ta bayyanashi a matsayin nata ita kadai sannan kuma me buhu-buhu amma kamar yanda tace na Masara, bana 'yan mata ba kamar yanda aka sanshi a baya ba.
Gadai abinda Mansurar ta rubuta kamar haka:
"I was like " the heart belong to me n me alone " he was like hmmm ya zanyi da buhu buhun masara bana mata ba 🤣🤣😭🤣🤣😛😛😛. Danja wutan baya 🤣🤣. Mai buhu buhu Amma na masara da dawa 🤣🤣. Dan fari, son kowa ki wanda ya rasa 🤣🤣🤣. 💚💚💚. Chill my Dan auta 💃💃💃😛😛 daga Kai babu kowa. No second thought 🤣🤣🤣."

Wannan rubutu na Mansurah ya dauki hankulan mutane sosai yanda akayi ta mayar da martani kala-kala, ga wasu daga cikin ra'ayoyin mutane akan wannan kirari da Mansurar ta yiwa mijinta.
Muna musu fatan Alheri da kuma Allah ya kara dankon soyayya.

No comments:

Post a Comment