Monday, 20 November 2017

Shirin N-Power ya fitar da yanda mutum zai duba sunanshi yaga idan an daukeshi aikin a yau

A satin daya gabatane shirin nan na rage radadin talauci tsakanin matasa na gwamnatin tarayyawa watau N-Power, ya bayyana cewa yau litinin, wadanda suka nemi aikin na wannan shekarar ta 2017 zasu iya duba sunayensu suga idan suna cikin wadanda aka dauka aikin.

Tun a wancan lokacin mutane sunyi ta tambayar ta yaya mutum zai duba yaga cewa an zabeshi?

To a yau da safe shirin ya fitar da sanarwar yanda duk wanda ya nemi aikin zai duba sunanshi ko yana cikin wadanda aka dauka, kamar yanda bayanin yake a hotonnan na sama.

Allah yaba me rabo sa'a.

No comments:

Post a Comment