Friday, 17 November 2017

Shirin rage radadin talauci ga matasa, N-Power zai wallafa sunayen wadanda suka samu aikin na wannan shekarar ranar Litinin

Shirin gwamnatin tarayyarnan na tallafawa matasa kan rage radadin talauci watau N-Power ya fitar da sanarwar cewa ranar Litinin idan Allah ya kaimu watau 20 ga watan Nuwamba na shekarar nan da muke ciki zai dora sunayen wadanda sukayi nasarar samun wannan aikin na wannan shekarar.Saboda haka ya umarci mutane da su duba sunayensu da misalin karfe 11:30 na dare Idan Allah ya kaimu ranar litinin din.

Sai muce Allah ya bada sa'a.

No comments:

Post a Comment