Tuesday, 7 November 2017

Shugaba Buhari ya bude taron kiniyya da fasaha

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bude wani taron kwanaki uku na harkar kimiyya da fasaha da aka farayi yau gurin taro na kasa da kasa dake Abuja, taron wanda akawa lakabi da cewa zai habbaka tattalin arzikin Najeriya ta hanyar yin anfani da kayan kimiyya da fasaha da aka kirkirosu anan gida Najeriya ya samu halartar shugaban hukumar bukasa fasahar sadarwa ta zamani ta kasa(NITDA) Dr. Aliyu Isah Fantami da ministan harkar sadarwa Otumba Adebayo Shittu.Akwai sauran manyan ma'aikatan gwamnati da suka halarci gurin taron.

No comments:

Post a Comment