Tuesday, 28 November 2017

Shugaba Buhari ya lashe wani zaben gwaji da akayi tsakaninshi da Atiku akan waye zai zama shugaban kasa

A wata kuri'ar gwaji da shafinnan na kwarmato labarai me suna Sahara Reporter ya gudanar tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa daya bar jam'iyyar ta APC zuwa PDP, Alhaji Atiku Abubakar akan wa mutane zasu zaba ifan zabe yazo, Shugaba Buhari ne yayi nasara da gagarumin rinjaye.

A kuri'ar Atiku ya samu kaso 26 yayin da shugaba Buhari ya samu 49, wannan ya kara nuna cewa har yanzu mutanen Najeriya na tare da Muhammad Buhari.

No comments:

Post a Comment