Thursday, 30 November 2017

Shugaba Buhari zai kai ziyara kasar Jordan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara kasar Jordan ranar 2 da 3 ga watan Disamba, me kamawa, inda zai halarci taro kan yanda za'a magance harkokin ta'addanci, shugaban zai bayyana irin yanda ayyukan ta'addanci suka shafi Najeriya a gurin taron.
Gwamnonin jihohin Osun, Kogi da Naija ne tare da wasu ministoci zasu yiwa Buharin rakiya.

Wannan sakon yana cikin sanarwar da me taimakawa shugaban kasar akan harkokin watsa labarai, Femi Adesina ya fitar ayau.

No comments:

Post a Comment