Wednesday, 22 November 2017

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da kwamitin tantance kadarorin gwamnati da aka kwato: An gudanar da taron majalisar koli a ofishin matar shugaban kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da kwamitin tantance kudade da kadarorin da hukumomin gwamnatinshi suka kwato daga hannun mahandama a yau kamin daga baya aka fara taron majalisar zartarwa wanda aka sabayi duk ranar laraba.


Taron na majalisar koli na yau an yishine a dakin taro dake karkashin ofishin matar shugaban kasa saboda ainihin dakin taron da aka sabayin zaman majalisar nada wasu matsaloli da ake kokarin shawo kansu kamar yanda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment