Wednesday, 8 November 2017

Tsayuwar sama da awa guda Shugaba Muhammadu Buhari yayi yana jawabi a majalisar tarayya:hakan ya birge mutane musamman masoyanshi: Inda aka rika fadin baba ya samu lafiya

Wani labari da ya birge mutane musamman masoya shugaban kasa Muhammadu Buhari shine,  Shugaban yayi tsayawar mintuna 69, ko kuma ace awa daya da mintuna tara,a jiya. da ya je maja lisar Tararra inda ya gabatar da kasafin kudin badi, kuma yayi tsayawar ta dogon lokaci yana jawabi.


Wannan tsayawa da jaridar Daily Trust ta ruwaito tasa Mutane da dama musamman Masoya Buharin sun rika fadin cewa lallai baba lafiya ta samu kuma zai iya sake tsaya takara a zaben shekarar 2019 in Allah ya kaimu.

Wadanda suka raka shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa majalisar a Jiya wajan mika kasafin kudin sun hada da mataimakin kakin majalisa Yusu Lasun, shugaban majalisar dattijai Ahmad Lawal, shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da sauransu.

Shugaba Buharin yayi jawabine akan yanda aka aiwatar da kasafin kudin bana, 2017 da kuma yanda za'a aiwatar da kasafin kudin badi.

No comments:

Post a Comment