Monday, 13 November 2017

Shugaban kasar Amurka, Trump yace shugaban Koriya ta Arewa, Kim, ya zageshi ta hanyar ce mishi "tsoho" amma ya rama


 Wani abin dariya da daukar hankali ya faru tsakanin shugaban kasar Amurka Donald J. Trump da takawaranshi da suke yakin cacar baki watau Kim Jong Un na kasar Koriya ta Arewa, Trump dinne yayi wani rubutu a dandalinshi  na sada zumuna da muhawara na shafin Twitter inda yace."Me zai sa shugaban kasar koriya ta Arewa, Kim Jong Un yace min "Tsoho", wannan ai zagi na yayi, duk da ni kuma bazan taba kiranshi da "gajere, Kato ba"ayya(Na riga na fadi) nayi matukar kokarin ganin cewa mun zama abokai, watakila wataran zamu zama abokan!"


Trump dai da Kim suna caccar bakine akan shirin makamin kare dangi da kasar Koriya ta Arewar ke kerawa.

No comments:

Post a Comment