Wednesday, 15 November 2017

Sojoji sun kwace iko da kasar Zimbabuwe: Amma sunce ba juyin mulki zasu yi ba

Sojoji a kasar Zimbabuwe sun kwace iko da gidan talabijin na kasar sannan sun mamaye kan tituna a wani yunkuri da akewa kallon juyin mulkine, amma, a sanarwar da suka fitar, sunce ba juyin mulkine zasu yi ba, suna neman masu lafine da suka hana ruwa gudu a kasar dake zagaye da shugaban kasar, Robert Mugabe.Sun kara da cewa da zarar sun kammala komai zai dawo yanda yake, kuma shugaban kasar da iyalanshi suna cikin koshin lafiya, suna samun kulawa yanda ya kamata.

Saidai wasu masu sharhi akan al'amuran kasar sun bayyana cewa wannan juyin mulkine, kawai sojojin basa so su bayyana hakane saboda sun san cewa Duniya ba zata basu goyon baya ba.


No comments:

Post a Comment