Saturday, 4 November 2017

Sule Lamido ya kaiwa Muhammad Indimi ziyara a ofishinshi dake Abuja

Tsohon gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido kuma me neman tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019 idan Allah ya kaimu, karkashin tutar jam'iyyar PDP, ya kaiwa hanshakin attajirin dan kasuwa kuma sirikin shugaban kasa Muhammad Indimi ziyara a Ofishinshi dake Abuja jiya Juma'a. sun tattauna batutuwa daban-daban a Ofishin na Muhammad Indimi, kuma an hango mijin diyar shugaban kasa, wanda dama dane a gurin Muhammad Indimin watau Ahmad Indimi cikin tawagar baban nashi. Muna musu fatan Alheri.

No comments:

Post a Comment