Tuesday, 7 November 2017

Tamu tayi abin yabo:An karrama Amina Muhammad da lambar yabo ta wakiyar shekara a kasar Amurka

Wata jaridar kasar Amurka da ake kira da Foreign Policy ta karrama mataimakiyar majalisar dinkin Duniya, 'yar Najeriyarnan data fito daga yankin Arewa, Amina J. Muhammad da lambar yabo ta me sasantawa ta hanyar lumana/wakiliya ta shekara.

 Jaridar ta karrama Amina ne agurin wata liyafar cin abinci na musamman data shiryawa manyan mutane.

Muna taya Amina Murna da fatan Allah ya kara daukaka.

No comments:

Post a Comment