Saturday, 4 November 2017

Tauraron fina-finan Indiya, Sharukan ya kula Rahama Sadau

Fitacciyar korarriyar jarumar fina-finan Hausa Rahama Sadau tana cikin farin ciki da annashuwa sosai a yau domin kuwa fitaccen tauraron fina-finan kaar indiya wanda akewa lakabi da sarkin soyayya watau Sharukan ya kulata a dandalin shafin sada zumunta da muhawara na Twitter.

Yanda abin ya faru shine, shekaran jiya, ranar Alhamis Sharukan din yayi murnar zagayowar ranar haihuwarshi to Rahama Sadau ta aikamai sakon taya murna ta dandalinshi na sada zumunta da muhawara na shafin Twitter, inda ta rubuta "Ina tayaka murnar zagayowar ranar haihuwarka sarki Khan, ina sonka kuma ina girmamaka. (Mun) gode da kake saka mutane da yawa cikin farin ciki.
To yau sai gashi ya dawo mata da amsar sakon data aika mishi ta shafin twitter din, inda ya rubuta cewa " Zanyi kokarin karawa(akan abinda nikeyi). Nagode.
Ai kuwa tun bayan daya wallafa wannan sako a dandalin nashi na shafin Twitter mutane da dama sukayi ta nanatashi da kuma danna alamar son shi.
Itama Rahamar ta nuna matukar farin cikinta inda ta rubuta cewa " kai naji dadi(cikin mamaki), na gode da amsar da ka bani ranka ya dade"

No comments:

Post a Comment