Saturday, 11 November 2017

Tijjani Asase da diyarshi sunyi gasar iya gayu, wai kuma shine ya lashe gasar

Tauraron fina-finan Hausa Tijjani Asase kenan a wannan hoton tare da diyarshi me suna fanna,  jarumin yace a yaune sukayi gasar kwalliya, iya gayu shi da diyar tashi kuma wai shine ya lashe gasar da kuri'a 6 ita kuma tana da kuri'a 4.

Abin dai ya nisha dantar amma mutane da yawa da sukayi sharhi akan wannan batu basu yarda da sakamakon gasarba, inda sukace anyi magudi.

Gadai abinda Tijjani ya rubuta:
"
Salam barkanmu da asuba Asafiyar yaune akai gasar iya gayu wato wanka nida 'Yata fanna inda na kasata da kuriya 6 da 4 saikuta yani murna dan tsoho ya kada yarinya."

Kalli wasu daga cikin ra'ayoyin mutane akan wannan batu:

No comments:

Post a Comment