Thursday, 2 November 2017

Tottenham ta lallasa Real Madrid da ci 3-1 a wasan zakarun turai

Wasan Real Madrid da Tottenham ne yafi daukar hankali a cikin wasannin cin kofin zakarun turai da aka buga jiya, inda Tottenham din ta lallasa Real Madrid da ci uku da daya, wannan yaba mutane mamaki sosai duk da cewa shi wasa dama haka yake ba'a sanin ainihin abinda zai kasance sai an gamashi, anma mutane basu tsammanin koda za'aci Real Madrid a dura mata kwallaye har ukuba.Wannan dai shine mafi munun sakamako da kungiyar ta Real Madrid ta taba samu a cikin shekaru tara da suka gabata tun kamin a fito daga cikin rukunin da aka sakasu.
Da yake magana da manema labarai kocin Real Madrid Zidane yace, sun samu damar maki amma suka baras kuma a wannan wasa basu nuna irin kazar-kazar din da aka sansu dashiba, haka kuma yace 'yan wasan sun kasa nutsuwa su buga kwallo amma yace duk da haka bai damu ba, kuma duk abinda zai faru bazai taba damuwaba.

Ya kara da cewa rashin samun nasara a wasanni biyu ba abu bane me kyauba kuma yasan 'yan wasan a dakin canja kaya baza'a samu irin shewa da murnar da aka saba samuba a karahe yace kungiyar kwallo me kyauce tayi nasara akansu kuma yana tayasu murna akan wannan nasara, ita dama kwallo ta gaji haka, wataran kayi nasara wataran ayi nasara akanka

1 comment:

  1. I think this is an informative post and it is very useful and knowledgeable. therefore, I would like to thank you for the efforts you have made in writing this article. parque capricho madrid

    ReplyDelete