Monday, 20 November 2017

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na murnar zagayowar ranar haihuwarshi: Ya cika shekaru sittin da haihuwa

A yaune tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan yake cika shekaru sittin da haihuwa a Duniya, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tayashi murna, haka kuma sakonnin taya murnar zagayowar ranar haihuwartashi daga ciki da wajen kasarnan sai kara shigowa suke.


Abu daya da ake ta yabawa tsohon shugaban kasar akai shine mika mulki da yayi cikin ruwan sanyi a lokacin da ake ta dari-darin cewa watakila kasar ta wargaje, hakan yasa anata kitanshi da gwarzon diokradiyyar Afrika.

Muma muna tayashi murna.

No comments:

Post a Comment