Sunday, 19 November 2017

Wani Dan Majalisa Ya Kwashi Dumamen Tuwon Dawa Shi Da Al'ummarsa A Jihar Jigawa

Wani dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Kirikasanma a zauren majalisar jihar Jigawa, Honarabul Aliyu Muhammad Kirikasanma, ya kwashi dumamen tuwo tare da al'ummar mazabarsa a daidai lokacin da yake rangadin ziyartar al'ummar mazabarta sa.

Lallai da ace sauran 'yan siyasa haka suke shiga cikin jama'a suna jawo su a jiki to da watakila sun rika tausaya musu suna ayyukan da suka kamata kuma da an rage zaginsu wanda har wani lokacin suke shan ruwan duwatsu.
Labari daga rariya.

No comments:

Post a Comment