Saturday, 11 November 2017

Wani Inyamuri daga jihar Imo ya musulunta: Ya zabi sunan 'Yusuf'

Wannan wani Inyamurine daga jihar Imo da Allah ya azurtashi da hasken zuciya ya amshi kalmar shahada jiya Juma'a kamar yanda wani wanda shima musulmin inyamurinne ya wallafa a dandalinshi na sada zumunta da muhawara, shi dai wannan bawan Allah ya zabi sunan Yusuf bayan da ya yi kalmar shada.
Muna mai fatan Allah ya kara fahimtar dashi addinin musulunci kuma ya karo mana irinsu.

ko da a satin daya gabata an samu wata baiwar Allah me suna A'ishat Obi daga dai jihar ta Imo inda ta fito tace ina alfahari da kasancewata musulma , kuma ta karfafawa 'yan uwanta inyamurai gwiwa akan su fito su daina jin tsoron karbar addinin musulunci, kuma su tashi su nemi ilimin addinin.

No comments:

Post a Comment