Sunday, 5 November 2017

Wani malami a kasar Misra/Egypt yace mutum zai iya auren diyar daya haifa ba ta hanyar aure ba: Hakan ya jawo cece-kuce a Duniya

Wani malamin jami'ar Al-azhar ta kasar Misira/Egypt ya shiga kanun labaran Duniya bayan daya yi wata magana a wani bidiyo da yanzu haka yake ta yaduwa a kafafen watsa labarai da shafukan sada zumunta da muhawara na zamani, malamin me suma mazen al-serawi yace ne mutum zai iya auren diyar da ya aifa ba ta hanyar aureba(watau 'yar mutum ta gaba fatiha).Malamin yace Imam shafi'i ya fada cewa diyar da mutum ya haifa ta hanyar "zina" to a shari'ance ba diyarshi bace domin bazata amsa sunanshiba saboda haka zai iya aurenta.

Malamin yayi wannan maganane a gurin wani wa'azi daya gudanar tun shekarar 2012, amma sai yanzune ake watsa bidiyon kuma kafafen watsa labarai da dama sun buga wannan labarin inda wasu ke ganin wannan magana ta malamin salaf Mazen bata daceba.

Allah ya kara fahimtar damu addininmu.

No comments:

Post a Comment