Tuesday, 28 November 2017

Wani takalmin sojoji da aka kera a Zaria ya shiga cikin takalma mafi inganci na Duniya

Takalmin sojoji da wani kamfanin kera takalma dake garin Zariya me suna NILEST a takice, ya kera, ya samu shiga cikin takalman sojojin mafi inganci a Duniya. KAmar yanda Daily Trust ta ruwaito, Shugabar Kamfanin ta bayyana haka a lokacin da wasu daliban makarantar horar da sojoji ta kasa suka kai ziyara kamfanin.

Ngozi ta bayyana cewa a shekarar 2016 makarantar horar da kuratan sojoji dake Zariya ta basu kwangilar hada takalma guda dubu biyu wadanda sabbin sojoji zasu yi amfani dasu, ta ci gaba da cewa, sun kammala takalman akan lokaci, kuma hukumar sojan ta bayyana takalman a matsayin daya daga cikin mafi inganci a Duniya baki daya.

Tace wannan dalili yasa hukumar sojan, a wannan shekarar ta kara baiwa kamfanin kwangilar saje hada wasu takalman guda dubu uku, a karshe tayi kira ga sojojin da su rika amfanin da takalman kamfanin dan ya ci gaba da rike matsayinshi da daya a Najeriya

No comments:

Post a Comment