Monday, 13 November 2017

Wannan hoton na gwamnan jihar Rivers ya dauki hankula

Wannan hoton na gwamnan jihar River Nyesom Wike ya dauki hankulan mutane, a jiyane aka dauki hoton bayan da gwamnan ya halarci wani taron jam'iyyar PDP a jihar Enugu, hoton dai ya nuna gwamnan kamar yana jin bacci, wasu kuma da sukayi sharhi a hoton sunce wai yasha giyane ya bugu.


Amma wasu sun kareshi inda sukace ai me zirga-zirga da aiki irin na gwamna ba abin mamaki bane idan ma an ganshi yana jin bacci, haka kuma wasu sunce idan ma giyar yasha ai yana da hankalinshi yasan dai-dai yasan ba dai-dai ba.

No comments:

Post a Comment