Tuesday, 28 November 2017

Wasu kafafen watsa labari sun bayyana shugaba Buhari a matsayin tsohon shugaban kasa

Wasu kafafen watsa labarai sun bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin tsohon shugaban kasa a lokacin da suka wallafa labarin kaddamar da kwamitin da zai duba yiyuwar karin albashi da shugaban yayi a jiya, me baiwa shugaban kasar shawara ta fannin sabbin kafafen watsa labarai, Bashir Ahmad ya jawo hankulan wadannan kafafen da su gyara wannan kanun labarai da suka saka, a cikin wani sako daya rubuta yacewa, Muhammadu Buhari shine shugaban kasa Najeriya a yanzu.

Wannan abu ya jawowa wadannan kafafen watsa labarai Allah wadai, inda mutane suka rika cewa ko menene manufarsu ta wallafa irin wannan labari haka?No comments:

Post a Comment