Wednesday, 1 November 2017

"Ya kama Ace Sa'adiya Adam ta san kalmar MALL: 'Yan Najeriya basu san uzuriba">>Nafisa Abdullahi

Daya daga cikin batutuwan da suka jawo cece kuce a satin daya gabata shine kuskuren da jarumar fim dinnan Sa'adiya Adam tayi wajan fadar kalmar turanci ta MALL yayin da take kokarin gayyatar masoyanta zuwa kallon wani sabon fim da ya fito, maimakon tace MALL sai tace MALT, wannan abu yasa wasu da yawa suka mata dariya duk da cewa wasu sun mata uzuri,  idan baka karanta labarinba ko kuma baka kalli bidiyonba to danna nan .Bayan da abin yayi yawa Sa'adiya ta janye bodiyon daga dandalinta na sada zumunta da muhawara sannan kuma ta sake yin wani bidiyon inda ta roki mutne da su rika yi musu uzuri sannan kuma ta gyara kuskuren da tayi.

Fatacciyar jarumar fina-finan Hausa Nafisa Abdullahi tayi tsokaci akan bidiyon bayar da hakurin da Sa'adiya tayi inda tace babu lallai sai ta ba mutane hakuri domin kuskurene kowama yanayi sannan kuma duk irin bayanin da zatayi 'yan Najeriya ba zasu taba mata uzuri ba zasu.Haka kuma Nafisa Abdullahi ta kara da cewa yafa kamata ace Sa'adiyar tasan wannan kalma ta MALL amma idan ma bata saniba ba wani abu bane tunda dai turancinnan ba yaran mu bane.

No comments:

Post a Comment