Wednesday, 29 November 2017

Ya kera keke me tafiya akan ruwa bayan da ya jingine karatun boko

Wannan wani bawan Allahne dan kasar Ghana daya kera keke me tafiya akan ruwa, mutumin ya bayyana cewa ya fara karatu, har yakai shekarar karshe a makarantar jami'a amma saboda wasu dalilai da be bayyana ba, ya jingine karatun.

Dangane da wannan keke daya kera kuwa yace ya fara aikinshine tun watan Agustan bara.
Irin wannan abu yana nuna cewa bawai sai a makarantar boko kawai ake samo basirar yin abubuwan cigaban rayuwaba, wasu Allahne kawai ya albarkacesu da yin tunanin kirkira, shiyasa karka rena mutum wai dan kana ganin ka fishi ilimi.


No comments:

Post a Comment