Sunday, 19 November 2017

Zaka iya cin abincin da me cutar Kanjamau ya dafa?: Ga wani gidan cin abinci da aka bude, masu cutar kanjamaune kawai ke aiki a ciki

Wani asibiti dake kula da masu dauke da cutar Kanjamau/HIV/Aids a kasar Canada me suna Casey House ya bude gurin sayar da abinci wanda masu dauke da cutar Kanjamau din kawai ya dauka aiki, suke dafa abincin, da sayarwa da mutane.


Gurin sayar da bincin me suna Junes Eatery, kamar yanda Asibitin ya bayyana, ya bude shine kuma ya dauki ma'aikata masu dauke da cutar Kanjamau kawai dan ya kawar da irin kyamar da mutane kewa masu dauke da cutar.

Bayan da aka yita kokarin wayar da kan mutane akan cutar kanjamau, da yawa an fahimci cewa ba'a daukarta ta hanyoyin cin abinci tare da me cutar ko yin amfani da bandaki daya ko kuma gaisawa dadai sauransu. To amma cin abincin da me dauke da cutar ya dafa, ba kowa bane zai iya.
Kamar dai yanda rahotanni suka bayyana a jikin bangon gurin cin abincin anyi rubuce-rubuce kamar haka: Ana daukar cutar kanjamau ta hanyar cin abincin da me dauke da cutar ya dafa: A' a babu wanda yace haka. Dadai sauran maganganu masu wayarwa da muutane kai akan wannan cuta.

Wanda ya assasa gidan cin abincin yace yana fatan gina irinshi a kasashen Amurka da Ingila.

No comments:

Post a Comment