Sunday, 26 November 2017

Zuwan dan shugaban hukumar kula da jami'o'in Najeriya karatu kasar waje ya jawo cece-kuce

Wannan shugaban hukumar kula da jami'o'in Najeriyane, NUC a takaice, Adamu Abubakar Rasheed tare da danshi wanda ya kammala karatun digiri da digirgir a wata jami'ar kasar waje, 'yan Najeriya da dama, ta kafafen sada zumunta na yanar gizo, sunyi Allah wadai da wannan bu.


Wasu dai sunce wannan kwata-kwata bai kamata ba, ace dan shugaban hukumar kula da jami'o'in Najeriya wai danshi ya fita yayi karatu a jami'ar kasar waje, bayan ga 'ya'yan talakawa nan a jami'o'in Najeriya sunata fama da karatu cikin yanayin marar kyau a kusan mafi yawancin jami'o'in?
Wannan lamari dai ya dauki hankulan mutane sosai inda har aka fara kira cewa, shugaban hukumar jami'o'in ya sauka daga mukaminshi, saboda wannan alamace ta rashin kishin kasa da talaka.


No comments:

Post a Comment