Thursday, 28 December 2017

Abdulmumini Jibrin ya bayyana abinda suka tattauna da shugaban kasa a ganawar da sukayi yau

Dan majalisar tarayya da aka dakatar, Abdulmumini Jibrin dake wakiltar mazabar Kiru da Bebeji daga jihar Kano ya bayyana abinda auka tattauna da shugaban kasa, Muhammadu Buhari a ganawar da sukayi yau, Abdulmumini Jibril yace, ganawar tasu akan maganar dakatar dashi da akayine a majalisar.Gadai sakon daya fitar a dandalinshi na sada zumunta da Muhawara kamar haka:

"
Maigirma Hon Abdulmumin Jibrin Kofa Maliya Tare Da Maigirma Shugabankasa Muhammadu Buhari Yau Afadar Gwamnatin Tarayya Abuja.

Maigirma Abdulmumin Kofa Yagana Da Shugabankasa ne Inda Suka Tattauna Muhimman Batutuwa Game da Harkokin Siyasa da Cigaban Tattalin Arzikin Kasa Dakuma Dakatar da Mazabarsa Ta Kiru Da Babeji Daga Zauran Majalisa.
"

No comments:

Post a Comment