Saturday, 16 December 2017

"Abin a jinin gidanmu yake": Rahama Sadau ta taya dan uwanta daya kammala karatun jami'a, ya kuma samu kyautar mafi shahara a tsakanin dalibai murna

Fitacciyar korarriyar jarumar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau ta taya dan uwanta Abba Sadau daya kammala jami'ar Umar Musa 'Yar Adua dake jihar katsina murna, a bikin da sukayi na murnar kammala karatun, shida abokanshi, an baiwa Abban kyautar karramawa ta wanda yafi yin fice a tsakanin daliban.Wannan yasa Rahama ta samu karin kaimin tayashi murna inda ta bayyana cewa abin a jinin gidansu yake. Muna tayashi murna da fatan Allah yasa ya amfaneshi da sauran al'umma baki daya.

No comments:

Post a Comment